Ronaldo baya samun isasshen bacci
Mai horas da yan wasan kasar Portugal Fernando Santos ya bayyana cewa dan wasan sa Cristiano Ronaldo ya kasa samun isasshen bacci tun bayan da ya zubda bugun fenarati lokacin wasan su da kasar Austria inda aka tashi wasan kunnen doki babu wanda yaci wani.
Cristiano Ronaldo
Duk da hakan dai dan wasan gaban na kulob din Realmadrid ya kafa tarihi amatsayin dan wasan da ya buga ma kasar sa wasanni 128. “Tun bayan da zubda kwallon nan bai sake samun isasshen bacci ba.” Inji mai horas da kasar ta Portugal.
Kafar yada labarai ta Sky Sports ma dai ta ruwaito cewa dan shekara 31 din yana fuskantar rashin katabus din da yafi na koyaushe a tsawon lokacin da yayi yana buga kwallo a inda kasar tasa take fuskantar kora tun a zagayen farko na gasar.
Karanta: Jonathan ya kasa samun kyautar Mo Ibrahim
Yanzu haka dai kasat ta Portugal tana da maki 2 ne kacal bayan kunnen doki har sau 2 da ta buga kuma tana a matsayi na 3 ne a rukunin ‘F’ inda kuma take bayan kasar Hungry da take ta farko da maki 4. A ranar laraba ne dai Portugal din zata kara da kasar Hungry inda kuma idan ta doke ta zata jagoranci rukunin amma kuma masu sharhi suna ganin abu ne mai matukar wahala. Shi dai Ronaldo ana sa ran zai taka muhimmiyar rawa a wannan wasan.
The post Ronaldo baya samun isasshen bacci appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Nigerian newspapers.
